Cikin matakan da za’a dauka har da ganowa tare da tarwatsa kwarababbun jiragen masu safarar mutanen da ke kokarin gujewa yaki da matsalolin Afrika da Gabas ta Tsakiya da kuma yankin Asiya.
Shugabannin za su ninka kudaden gudunmawa ga kungiyar tarayyar Turai domin yin sintiri a kan iyakokin teku da kuma kokarin tsugunar da ‘yan gudun hijira daga kasashen gabar tekun Madetareniyar kasashen Turai.
Shirin tsugunar da ‘yan gudun hijirar ya yi tanadi ga mutanen kimanin guda 5,000 wadanda wani bangare ne na jimillar ‘yan gudun hijirar da suka tsallaka Turai.
A yanzu haka mutane a tsibirin Malta dake kan yankin tekun Madetareniya sun taru don yin jana’izar mutanensu 24 da suka mutu a hatsarin ranar Lahadi.
Cikin wadanda suka halarci wajen makokin har da Shugaban kasa da Firamistan Malta da kwamishinan Kungiyar Tarayyar Turai na harkokin shige da fice tare da ma wasu jami’an kasar Italiya.