Sojojin 'kawance da Saudi ke jagoranta sun kai sabbin hare-haren jiragen sama a Yemen a jiya Laraba, ‘yan sa’o’i bayan sanarwar tsagaita ruwan bama-baman da aka kwashe wata guda ana yi.
Hare-haren jiragen saman sun shafi sansanonin ‘yan tawayen Houthi a birnin Taiz da kuma gabar birnin Aden da ke kudancin kasar, a daidai lokacin da ake cigaba da fafatawa ta kasa tsakanin 'yan tawayen da magoya bayan shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi.
Bayan da ‘yan tawayen suka kwace sansanin daga hannun dakarun dake marawa shugaba Abd-Rabbu Hadi baya, an kai hari ta sama a wurin.
Ranar Talata Saudi Arabia ta fadi cewa ta kawo karshen hare-haren da ta kwashe wata daya tana kai wa da niyyar dakile dannawar da ‘yan Houthi ke yi, amma zata maida hankali akan neman masalaha a siyasance da ka iya hadawa da daukar matakan da zasu hana ‘yan tawayen na Houthi mallaka ko yin amfani da makaman sojojin Yemen.
A halin da ake ciki kuma, ‘yan tawayen na Houthi na kiran da a koma kan teburin shawarar da Majalisar Dinkin Duniya ke daukar nauyinsa don warware rikicin na Yemen.
A birnin New York mai magana da yawun Majalisar Stephane Dujarric yace, a shirye take wajen 'daukar kowane matsayi na ganin an samu sasantawa kan rigingimun na Yemen.