Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka da Asiya Sun Fara Taronsu Yau a Indonesia


Wasu shugabannin kasashen Afirka da Asiya tare da shugaban Indonesia mai masaukin baki Joko Widodo mutum na biyu daga dama.
Wasu shugabannin kasashen Afirka da Asiya tare da shugaban Indonesia mai masaukin baki Joko Widodo mutum na biyu daga dama.

Shugabannin Afirka da Asiya zasu yi taronsu na karfafa dangantaka tsakanin kasashen nahiyoyin biyu.

Shugabannin kasashen Asiya da na Afirka sun fara isa Jakarta, babban birnin kasar Indonesiya, don gudanar da babban taron kasashen Asiya da Afirka na kwanaki 2, wanda ake farawa yau Laraba.

Babban taron, wanda manufarsa ita ce, karfafa dangantaka tsakanin kasashen Asiya da Afirka, ya yi kama da babban taron shekarar 1955, wanda ya share fagen kafa kungiyar 'yan baruwanmu a zamanin yakin cacar baka.

Taron na 1955, wanda aka yi a Tsibirin Java, ya janyo kasashen da yawancinsu ba su jima da samun 'yancin kai ba, bayan sun jima karkashin mulkin mallaka da kuma mamayar kasashen waje.

Shugabannin kasashe sama da 30 ne ke shirin halartar wannan babban taron, ciki har da Shugabannin kasashen China, da Japan da Brunei da Malaysia da Myanmar. Ba zato Shugaban Afirka Ta Kudu ya soke halartar taron saboda tashin hankali mai nasaba da kin baki a kasarsa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG