Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Hallaka Mutane Bakwai a Somaliya


Baraguzan motar da bam ya tashin a cikinta a Mogadishu
Baraguzan motar da bam ya tashin a cikinta a Mogadishu

Kungiyar al-Shabab ta tayarda wani bam a wani fitaccen gidan cin abinci inda jami'an gwamnati suka fi halarta a birnin Mogadishu babban birnin Somaliya

Akalla mutane 7 ne suka mutu a Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya, bayan da bam ya tashi cikin wata mota a jiya Talata a harabar wani fitaccen wurin cin abinci, daidai lokacin cin abincin rana.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito wani mai magana da yawun kungiyar al-Shabab na cewa kungiyar mayakan ce ta kai harin. Wasu mutane akalla 8 kuma sun sami rauni a fashewar, wadda aka auna ta kan gidan cin abinci na Banoda, wanda nan ne jami'an gwamnati da sauran ma'aikatan Fadar Shugaban kasar Somaliya su ka fai cin abinci.

Wannan ne mummunan hari na hudu da al-Shabab ta kai a Somaliya cikin kwanaki hudu.

A halin da ake ciki kuma, gwamnatin Amurka ta ayyana wasu kusoshin al-Shabab biyu a zaman 'yan ta'adda a hukumance. Dayan shi ne Ahmed Diriye, wanda ya zama babban shugaban al-Shabab bayan da dadadden shugabanta Ahmed Godane, ya mutu a wani harin da jirgin saman Amurka mara matuki ya kai a watan Satumba.

Na biyun, wato Abdirahim Mohammed Warsame, ya taka rawa sosai a kungiyar Amniyat, wadda wata bangare ce ta kungiyar ta al-Shabab, wadda ta kai wani hari kwanan nan a wata Jami'ar kasar Kenya, da ya yi sanadin mutuwar dalibai 150.

XS
SM
MD
LG