Al’umar Fulani a Najeriya ta nuna damuwa kan yadda ake yi musu kudin goro wajen danganta su da matsalar sace-sacen mutane da ake yi a wasu sassan kasar.
Yayin wani taro da kusoshin kungiyar Miyetti Allah suka yi a Abuja, babban birnin Najeriya, mambobin da suka fito daga sassan kasar, sun tattauna kan ƙalubalen da Fulani makiyaya ke fuskanta a kasar musamman ma ta fuskar tsaro.
Kamar yadda rahotanni ke nunawa, mafi akasarin hare-haren garkuwa da mutane da ake yi a Najeriya, akan danganta su ne da al’umar Fulani.
Sai dai Sakataren kungiya na kasa Malam Baba Usman Ganjarma ya nuna ba haka lamarin yake ba.
“Yau bafulatani a Najeriya cikin tashin hankali yake ta fuskar tsaro, bayan shi abun ya fi shafa kuma yau kusan ko wani kabila yana ganin kamar shi dan ta’adda ne, ba ka tara al’ummar kabila guda ga baki daya kamar na wanda yawansu ya kai kusan kashi 30 cikin dari na al’umma Najeriya ka hada su duka ka ce yan ta’ada ne to idan ka yi haka to ba ka yi adalci ba”. In ji Ganjarma.
Wannan batu na zuwa a daidai lokacin da kungiyar ta samu sabon shugaba bayan murabus din da Muhammadu Kiruwa ya yi a wani yanayi da ba a saba gani ba a matsayin shugaban kungiyar.
Alh. Mohammadu Mafindi Ummaru Dan Buran dake neman takarar shugabancin kungiyar ta kasa, ya bayyana cewa rashin shugabanci ya haifar da halin kunci da al’ummar Fulani ke ciki.
Sai dai a cewar Sabon shugaban rikon kwarya na kungiyar Alh. Hussaini Yusuf Bosso, dole sai an kara kaimi wajen ilimantar da al’umma don samun mafita.
Tsohon ministan matasan a Najeriya Solomon Dalung wanda shi ma ya samu halatar taron, ya shaida wa Muryar Amurka cewa sai ana hukunta masu laifi tare da ba da karfi ga shugabanin gargajiya wajen tafiyar da al’amuran al’ummarsu.
A karshe dai ana fatan samun dauwamamman mafita da shugabanci na gari dake zama kalubalen da Fulani makiyayan ke fuskanta a Tarayyar Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim daga Abuja, Najeriya: