'Yan kasuwa daga kudanci da arewacin kasar Najeriya da kasashe dake makwaftaka da Najeriya suke saye da sayarwa a kasuwar.
Sakataren kungiyar masu sayarda kayan marmari ta Najeriya reshen jihar Kano Ismaila Saidu Koki yace kamar abarba sukan samu motoci kusan arba'in kullum.Mutane daga jihohi daban daban suke zuwa sayen kayan. Ita kuwa kankana idan ta kama sukan sauke motoci hamsin a rana guda. Mutane daga Legas ko Fatakwal suna zuwa su yi lodin kayan marmarin daga kasuwar. A kullum ana harkar nera miliyan hamsin.
Wani Obi Maikwakwa yana cikin masu kawo kaya daga birnin Legas. Shi yana kawo kwakwa ne cikin tireloli daga Legas. Yayi kimanin shekara goma sha biyar yana kawo kwakwa Kano. Yace a wata guda sukan kawo tireloli kusan talatin.
Shi ma Joseph daga jihar Binuwai yace yana kawo kaya daga Katsina-Ala kuma ya kwashe shekaru da dama yana kawo kayan.
Ahmed Yusuf Ibrahim daya daga cikin masu sayen kaya daga hannun fatake su sayarwa kananan 'yan kasuwa. Yace idan sun bude mota suna ba wadanda zasu shiga gari su sayar . Bisa ga ka'ida sukan basu kwana biyu ko uku kafin su kawo kudinsu.
Duk da rawar da kasuwar ke takawa wurin habaka tattalin arzikin jama'a daban daban sakataren 'yan kasuwan Ismaila Saidu Koki yace akwai kalubale da suke fuskanta. Abun da ya fi ci masu tuwo a kwarya shi ne rashin magudanar ruwa da kuma isasshen wurin ajiye motoci. Yanzu suna samun cunkoson motoci. Kasuwar kuma na bukatar wurin tara shara. Kana suna neman a ingatawa kasuwar tsaro.
Ga rahoton Mahmud Kwari.