WASHINGTON, DC —
Hukumomi a matakai daban daban suna daukan matakin tsaftace muhalli domin kada a samu barkewar cututtuka a lokacin damina da kuma gyara magudanun ruwa domin yin rigakafin barnar ambaliyar ruwa
Alhaji Yakubu Mohammed Bello babban manajan tsaftace muhalli ta jihar Neja yayi karin haske akan matakan da suke dauka a daidai wannan lokacin da damina ke karatowa. Yace damina takan zo da wasu abubuwa da dama kamar ciyawa da ambaliyar ruwa. Yace wata mai zuwa zasu fara yanke ciyawa domin kada ta taso ta mamaye gidaje. Dangane da magudanar ruwa sun rubutawa gwamnan jihar ya tabbatar masu da abubuwan da suka tsara zasu yi. Suna bukatar kudi su yashe duk magudanan ruwa dake cikin garin Minna.
Gwamnantin jihar tace tana kashe nera miliyan ashirin kowane wata domin aikin kwashe shara a jihar kamar yadda babban sakataren ma'aikatar kula da muhalli ta jihar Umar Muhammed Bawa ya bayyana. Kwashe sharar da ake yi a duk fadin jihar ya hada da duba gari domin a tabbatar mutane suna yin abun da ya kamata domin kada su kawo cuta.
To saidai Alhaji Muhammed Bello yace babbar matsalarsu a jihar ita ce halayen mutane. Yace suna anfani da radiyo da telibijan suna fadakarda mutane akan mahimmanci tsafta da tsaftace muhalli. Har ma suna anfani da motar shela suna bi anguwa anguwa suna fadakarwa. Yace duk da haka mutane basa ji. Yace sai ka ga mutum ya sha mangwaro ko lemu sai ya jefar da kwallon ko bawon akan hanya duk da tanadin wuraren da za'a sa shara a koina har ma da gefen hanyoyi.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.