Laraba ce ranar da aka kara domin karfafa gwiwar masu son zuwa rumfunan zabe a dai-dai lokacin jami’an gwamnati ke karfafa gangamin gwiwar da su fita su jefa kuri’arsu a zaben da ake kyautata cewar tsohon jagoran rundunar sojojin kasar Misra Abdul-Fatah el-Siissi ne zai kai ga samu nasara.
Masu fashin baki sun bayyana cewar ba'a zaci samun karancin masu jefa kuri'a a kwanaki biyun farko da aka kebe domin gudanar da zaben ba, hakan ne yasa hukumar zaben kasar tayi karin rana guda,amma duk da hakan ba'a cincirindon masu son kada kuri'a a layin rumfunan zaben a yau ba.
Rashin fitowar masu kada kuri'a masu yawan ne yasa hukumar zabe kara lokaci domin baiwa kowa isasshen lokacin zuwa yin amfani da damarsa ta zaben wanda yake so.