Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba A Tilastawa Abdullahi Adamu Yin Murabus Ba - APC


Abdullah Adamu
Abdullah Adamu

Jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya ta ce ba wanda ya tilastawa Sanata Abdullahi Adamu yin murabus daga shugabancin jam'iyyar.

ABUJA, NIGERIA - APC ta bayyana haka ne bayan kammala taron shugabannin gudanarwa na jam'iyyar da ya dora mataimakin shugaban jam'iyyar na Arewa a matsayin shugaban wucin gadi.

A hirar shi da Muryar Amurka, Daraktan labaru na jam'iyar APC Bala Ibrahim ya jaddada cewa, bisa radin kai Abdullahi Adamu ya mika takardar murabus don haka ma bai halarci taron na nada zaben shugaban wucin gadi ba..

Abdullahi Adamu wanda ya hau mukamin sakamakon goyon baya da ya samu daga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba ya fargabar wata barazana ko kalubalen siyasa.

Masana siyasa sun dade da hango ba za a samu jituwa tsakanin Sanata Adamu da shugaba Tinubu ba bisa hannun riga da su ka yi gabanin zaben fidda gwani na ‘dan takarar jam'iyyar.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:

Ba A Tilastawa Abdullahi Adamu Yin Murabus - APC.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG