ABUJA, NIGERIA - Wannan dai ba shi ne karon farko da aka fitar da jerin sunayen "sababbin Ministocin" ba tun bayan rantsar da Bola Tinubu Shugaban kasa.
Duk da ana sa ran Shugaba Tinubu zai mika sunayen Ministocinsa ga Majalisar Dattawa nan ba da dadewa ba; amma wadanda su ka bayyana zuwa yanzu sun zama tamkar na fatan alheri ne ko yada farafaganda da wasu ke yi don tallata sunayen wasu gwanayensu.
Abun da ya fito fili a sunayen da a ka yayata da ba sunan wanda ya fitar da sanarwar kamar yadda ake gani a bayanai masu tushe daga daraktan labarai na ofishin Sakataren Gwamnati Willie Bassey ko ma kakakin Shugaba Tinubu, Dele Alake.
A hirar shi da Muryar Amurka, dan kwamitin gudanarwa na APC Dattuwa Ali Kumo ya ce ba bukatar gaggawa daga wadanda su ka yada bayanan marar sa tushe amma jerin hakika na tafe.
Za a jira a ga wadanda za su zama Ministocin Gwamnatin Tinubu da a ka ce 'yan siyasa za su ci gajiya kuma za a yi la'akari da gudunmawa daga jiha ko shawarar gwamnoni maimakon yadda tsohon shugaba Buhari ya nada Ministocin sa bisa ga wadanda ya sani ko ya gamsu ya yi aiki da su.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:
Dandalin Mu Tattauna