Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddama Na Neman Kaurewa Tsakanin Gwamnan Jihar Jigawa Da Masu Ruwa Da Tsaki A Jam’iyyar APC


Sabon Gwamnan Jigawa
Sabon Gwamnan Jigawa

Rashin samun daidaito game da wanda zai jagoranci majalisar jihar ta Jigawa karo na takwas, shi ne ya haifar da tsaiko wajen rantsar da sabbin ‘yan majalisar ranar Talata.

JIGAWA, NIGERIA - Takaddamar ta nemi kaurewa ne tsakanin gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar cikin su kuwa har da tsohon gwamnan jihar Badaru Abubakar, dangane da zaben shugaban majalisar dokokin jihar.

Bayanai da muka tattara daga kafofin masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC a jihar ta Jigawa sun nuna mutane uku ne ke takarar shugabancin majalisar dokokin jihar, cikin su kuwa har da tsohon shugaban da ya kammala wa’adin sa a watan jiya, wato Hon. Idris Garba Kareka.

Rahotanni sun ce tsohon gwamna Badaru Abubakar da wasu kusoshi na Jam’iyyar na goyon bayan tsohon shugaban ya yi kome, yayin da sabon gwamna Malam Umar Namdi ke son a sami sabon hannu.

Amma, sakataren labarai na Gwamnan jihar Malam Hamisu Mohammed Gumel ya ce “ko kadan gwamma Malam Umar Namadi ba shi da hannu akan wa ye zai zama shugaban majalisar dokoki, saboda hurumi ne na majalisar kawai kuma majalisa bangare ne mai cin gashin kan ta a bisa tanadin kudin tsarin mulkin kasa”.

Ko da yake, an yi tarukan masu ruwa da tsaki iri-iri domin samun dai-daito, amma an gagara cimma matsaya, al’amarin da ya sanya tilas zaben sabon shugaba da rantsar da sabbin ’yan majalisar faskara a Talatar nan.

Ga alama wannan takaddamar ta kara jefa ‘yan majalisar dokokin ta Jigawa cikin yanayi na rudani.

Hon. Mohammed Kabiru Ibrahim sabon ‘dan majalisar dokokin mai wakiltar mazabar Birnin Kudu a karkashin inuwar Jam’iyyar PDP ya ce “Ka san ni sabon ‘dan majalisa ne wanda nake jira a rantsar da ni, gaskiya ba zan iya cewa, ga abin da yake faruwa ba, da ance za’a rantsar da mu 13 ga wata, yanzu kuma ance 14 ga wata, amma dai ko ma menene ba zai rasa nasaba da batun wa ye zai zama shugaban majalisa ba”.

Rashin kaddamar da majalisar ne ya sanya wasu matasa suka gudanar da zanga-zanga zuwa gidan gwamnati a Dutse da kuma harabar majalisar dokokin.

Sai dai bayanai na nuni da cewa, nan gaba a yau ne ake sa ran za’a kaddamar da majalisar bayan da gwamnan jihar ya aika wasikar kaddamarwar, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya shata.

Saurari cikakken rahoto daga Mahmud Ibrahim Kwari:

Takaddama Na Neman Kaurewa Tsakanin Gwamnan Jihar Jigawa Da Masu Ruwa Da Tsaki A Jam’iyyar APC.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG