Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hasashen Saukar Shugaban APC Abdullahi Ta Tabbata


Senator Abdullahi Adamu
Senator Abdullahi Adamu

A hirarsa da wakilin Muryar Amurka, daraktan yada labarai na jam’iyyar APC, Bala Ibrahim, ya ce mataimakin shugaban jam'iyyar na arewa Sanata Abu Kyari ke jagorantar jam'iyyar.

Hasashen saukar shugaban jam'iyyar APC Abdullahi Adamu daga mukamin sa ta tabbata bisa la'akari da taron majalisar gudanarwa na jam'iyyar da ke gudana yanzu haka ba tare da shugaban ba.

Kazalika an hana sakataren jam'iyyar shiga dakin taro.

A hirarsa da wakilin Muryar Amurka, daraktan watsa labarai na jam’iyyar, Bala Ibrahim, ya ce mataimakin shugaban jam'iyyar na arewa Sanata Abu Kyari ke jagorantar jam'iyyar.

An fahimci Abdullahi Adamu ba ya dasawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu saboda bai mara masa baya a lokacin zaben fidda gwani ba.

Abdullahi Adamu ya mara baya ga tsohon shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan don samun tikitin APC inda Bola Tinubu ya samu gagarumar nasara.

Saurari hirarsu a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG