Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hankali Ya Koma Kan Nada Sabbin ‘Yan Majalisar Zartarwa Da Tinubu Zai Nada  


Ibrahim Kabir Masari
Ibrahim Kabir Masari

Biyo bayan sauke akasarin manyan jami'an tsohuwar gwamnatin da ta shude ta Buhari, yanzu hankali ya koma kan nada majalisar zartarwa ta sabuwar gwamnatin Bola Tinubu.

ABUJA, NIGERIA - Rahotanni na nuna cewa masu neman mukaman minista da manyan masu ba da shawara na kamun kafa don samun gurbi a gwamnatin shugaba Tinubu.

Mukarrabin shugaba Tinubu, wanda ya yi rikon mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023 Ibrahim Kabir Masari, ya ce ya na da kwarin gwiwa za a yi sabon zubi a wajen mukaman.

Masari ya ce duk da cewa wasu da dama a tsohuwar gwamnatin Buhari na bin kafa don sake dawowa kan kujera, hakan na da wuya ainun.

"Duk wanda ya rike mukami a tsohuwar gwamnatin Buhari ya dace ya koma gefe ya rungumi wata sana'ar don ba wa wasu damar gwada tasu basirar," a cewar Masari.

Lauya mai zaman kan sa a Abuja Auwal Aldulkadir Albarudi, ya shawarci shugaba Tinubu da ya raba gwamnatinsa da jami'an gwamnatin Buhari, don hakan ne zai ba shi damar nada nasa mutanen don samun sauyi daga wadanda a ke zargi da almundahana.

In za a tuna tsohon shugaba Muhammadu Buhari bai yi alwashin tsaya wa mutanen sa ba, abinda kai tsaye ke nufin kowa ya debo da zafi bakin sa.

"Duk wanda ya neme ni na ba da wata shaida a kan sa a kotu to ko waye ya kuka da kan sa," inji Buhari.

Tsohon shugaban dai na London da wasu mafi kusaci a mukarrabansa, wadanda in ka gan su a wuri to ba mamaki tsohon shugaban na kusa.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-hikaya:

 Hankali Ya Koma Kan Nada Sabbin ‘Yan Majalisar Zartarwa Da Tinubu Zai Nada .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG