Jihar Adamawa ta mayar da martani ga kalamun Farfasa Jega. Jihar ta ce biri fa ya yi kama da mutum a kalamun Farfasa Jega. A martanin da ta bayar ta bakin daraktan yada labaran gwamna Maryam Ahmed Sajo ta ce kalaman shugaban hukumar zaben na fa tada hankali matuka. Don haka ta ce da wata makarkashiya da ake son kullawa. Ta ce basu ne Allah ba domin suna da masaniya wai ba za'a yi zabe ba domin dokar ta baci.Ta ce doka ta ce ta wata shida ake yi kana idan abubuwa basu gyaru ba a kara wa'adin wata shida shi ke nan dokar ta kare. An riga an yi wa'adi na daya. Yanzu ana kan na biyu. Bayan an gama na biyu akwai watanni shida har sau uku. Don haka babu wata dokar ta baci kuma.
Idan dai ba su suke haddasa tashin hankali ba kuma ba zasu bar yin hakan ba to shi ne zasu ce sun san har zuwa lokacin zabe dokar ta baci na nan. Ya ce suna fata nan da wata shida an samu daidaito.
Ga 'yan siyasa irin su Dr Umar Ardo wani jigo a jam'iyyar PDP kuma tsohon dan takarar jam'iyyar a jihar na ganin akwai abun dubawa a kalamun hukumar zaben. Ya ce ba zasu yadda a ce basu da hannu wurin zaben shugaban kasa da gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi ba. Dole ne a kare dokar ta baci a watan Mayu mai zuwa.
Kungiyoyin da ba na siyasa ba sun yi gargadin a kai zuciya nesa musamman a wannan lokacin da siyasar kasar ke kara fadawa cikin wani mawuyacin hali. Malam Musa Uba na kungiyar sasanta al'umma ya ce kalamun shugaban INEC ka iya zama manuniyar abun da ka iya faruwa a zaben 2015. Ya ce dama an ce Farfasa Jega dan PDP ne to yanzu yana yiwa PDP aiki. Da kamata ya yi ya bari sai an kawo lokacin idan zaben ba zai yiwu ba to shike nan. Amma yanzu idan har aka kai lokacin ba'a samu zaman lafiya ba za'a ce dama su ne suke haddasa tashin hankalin.
Ibrahim Abdulaziz nada karin bayani.