Wakilin Muryar Amurka Ladan El-Hikaya ya taka zuwa hekwatar hukumar zaben wato INEC a takaice domin sanin gaskiyar maganar. Wani jami'in hukumar ya ce abun takaici ne da rashin fahimta wasu su dauka kamar su a hukumar basu yi niyar yi masu adalci ba bayan sun yi rantsuwa cewa a wannan tafiyar zasu yi adalci da yin nagarta da aiwatar da gaskiya. Bayan hakan ya ce abun da Farfasa Jega ya fada shi ne idan akwai tashin tashina ko dokar ta baci babu yadda zasu shirya zabe bisa ga doka.
Idan ana cikin halin tashin tashina mutane ba zasu samu karfin gwuiwa su fita su yi zabe ba.Ita ma hukumar zaben ba zata iya kare jami'anta ba. Idan ma sun nace su yi zaben ba zai yi tasiri ba kuma ba zai samu karbuwa ba. Abubuwan da ya kamata a fahimta da su ke nan ba wai ana son a yiwa wasu jihohi makarkashiya ba ne.
Ya ce a kokarinsu na son yin ingantaccen zabe sun gayyaci kwararru da wadanda suka yi anfani da wata naura ta musamman a Kenya suka kuma yi zabe cikin lumana sanadiyar yin anfani da naurar.
To amma ace wata kaddara ta hana a yi zabe a jihohin ana iya yin zaben fidda shugaban kasa ba tare da su ba? Jami'in ya ce ba'a kawo wannan halin ba yanzu. Amma sun yi imani kuma suna addu'a cewa kafin shekarar 2015 za'a kawo karshen tashin tashina da suka addabi jihohin uku. Idan ba'a yi zabe a jihohin uku yayin da wa'adin gwamnoninsu ya kare ko menene hukumar zaben zata yi? Za'a tura sojoji ke nan su cigaba da mulki ko menene shawarar hukumar. Jami'in ya kara da cewa ba'a kai wanna matsayin ba tukunna amma idan an kai ga hakan za'a yi komai bisa ga doka.
G karin bayani.