Buba Galadima ya ce yana da hurumin mayar da martani kan abubuwan da shugaban INEC ya fada. Ya ce sun sha cacar baki da gwamnati da ita INEC a kan irin wadannan abubuwa dake faruwa. Ya ce ya tabo irin wannan maganar a wata kasida da ya bayar a Kuru watan Satumbar shekarar 2012.
Dangane da cewa watakila ba za'a yi zabe a shiyarsu ba ya ce biri ya yi kama da mutum. Ya ce duk mutumin da maciji ya sareshi to idan ya ga tsumma zai daka tsalle. Al'ummar jihohin Borno da Adamawa da Yobe sun sha korafin cewa rikicin da ya ki ci ya ki cincewa a shiyarsa yana da haddasawa daga gwamnatin tarayya ko kuma jami'anta wadanda basa son rikicin ya kare domin suna hasashen zaben 2015 su kuma jami'an tsaro aka kashe makudan kudi a kansu.
Ya ce ana yaki a Mali amma kwanan nan aka yi zabe. Ana yaki a Liberia aka yi zabe. Ana yaki a Saliyau aka yi zabe. Yaki bai taba hana yin zabe ba. A jihar Kaduna gwamnatin tarayya sai da ta kame mutanen jam'iyyar adawa ta kashe wasu kana ta kafa dokar daurin talala aka yi zabe dole. Haka aka yi a Bauchi da wasu wurare. Wato don yanzu an ga akwai kuri'u miliyan biyar a jihohin uku kuma suna adawa da gwamnati Jonathan shi ya sa ana son a hanasu kada kuri'unsu.
Buba Galadima ya kara da cewa Farfasa Jega ya sani abun da ya ci Doma ba zai bar Awe ba. Kada ya gani domin ya zama karen farautan Jonathan su zasu sadakar da hakinsu domin hakin gwamnatin tarayya ne ta kawo zaman lafiya a koina a kasar. Al'umman jihohin nan uku ba zasu yi watsi da hakinsu ba ko ta halin kaka. Sai sun jefa tasu kuri'un a zaben shugaban kasa da na gwamnoni da na 'yan majalisu a zaben 2015. Duk abun da zai auku ya auku amma ba zasu yadda ba.
Nasiru Adamu El-Hikaya nada karin bayani.