Jam'iyyar ta kara da cewa ana musguna masu a kokarinsu na bude ofisoshi a jihohin dake karkashin ikon PDP. Tsohon kakakin majalisar wakilai Alhaji Aminu Masari wanda shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa ya ce maganar Rivers bata APC kadai ba ce. Magana ce da ta shafi kasar gaba daya domin yadda ake karya doka da cin zarafin mutane. A jihar ne 'yansandan Najeriya suka zama 'yansandan PDP. Ya ce zasu dauki duk matakan da suka dace su kawo gyara. Ya ce zasu kare dimokradiya da mutuncin 'yan jam'iyyarsu koina a Najeriya cikin matakin bin doka da oda da yin anfani da abun da doka ta tanada.
Dan majalisar wakilai Kawu Sumaila na ganin jam'iyyar APC ta kama hanyar karbe madafin iko daga PDP ta lashe zaben shekarar 2015. Ya ce idan da karantwa ake yi yanzu mutane sun gani sun kuma ji a jikinsu. Dole yanzu canji suke so, canji kuma a koina.
APC ta yi alkawarin magance rikicin cikin gida a Kano da Sokoto kuma zata fara yin ragistan sabbin 'yan jam'iyyar a watan gobe. Sanato Kabiru Gaya ya kara haske ya ce Dr Musa Kwankwaso shi ne shugaban APC a Kano kuma ya kamata Ibrahim Shekarau ya hakura domin a samu cigaba.
Ga karin bayani