Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ta Sharar Fagen Tattaunawar Trump Da Kim Jong Un


Wasu hotunan shugaba Trump na Amurka (Dama) da shugaba Kim na Korea ta Arewa (Hagu) da aka hada
Wasu hotunan shugaba Trump na Amurka (Dama) da shugaba Kim na Korea ta Arewa (Hagu) da aka hada

Ana ci gaba da sharar fage domin ganin an hada shugaba Donald Trump na Amurka da takwaran aikinsa, Kim Jong Un na Korea ta Arewa domin tattaunawa kan shirin makamin nukiliyan Korea ta Arewan.

A yau Lahadi, kafofin yada labarai a Korea ta Kudu, sun ruwaito cewa, wani babban jami’in kasar Korea ta Arewa ya kama hanyarsa ta zuwa kasar Findland domin haduwa da wasu tsoffin jami’an diplomasiyyar Amurka.

Hakan na faruwa ne, bayan da wata tawagar jami’an Korea ta Arewa suka kammala wata tattaunawa ta kwanaki uku, da jam’ian diflomasiyyar kasar Sweden.

Wannan tattawaunawa ana ganin ita za ta share fagen ganawar shugaba Donald Trump da takwaran aikinsa na Korea ta Arewa, Kim Jong Un.

Kamfanin dillancin labaran Yonhap na Korea ta Kudu, ya ruwaito cewa an ga mataimakin shugaban da ke kula da hulda tsakaninn Korea ta Arewa da yankin arewacin Amurka, Choe Kang II, a filin tashin jirage na kasa da kasa, da ke Beijing.

Daga baya anga ya shiga jirgi ya kama hanyarsa ta zuwa Findland.

Majiyoyi da dama sun bayyana cewa tsohuwar Jakadiyar Amurka a Korea ta Kudu, Kathleen Stephen, na daya daga cikin tsoffin jami’an diflomasiyan Amurka da za su gana da jami’in na Korea ta Arewa a kasar ta Findland.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG