Wani jami’in Amurka ya shaidawa Muryar Amurka cewa, Amurka na sane da lamarin, yana mai cewa “abind damuwa ne ainun” amma ‘yan Najeriya da dama sun samu damar barin kasar Ukraine a ranar Talata.
Hukumomin kasar Ukraine na baiwa mata da kananan yara 'yan kasar ta Ukraine da ke neman ficewa daga kasar fifiko, sai dai ba a bayyana yadda ake yiwa 'yan Afirka ya banbanta da na sauran 'yan kasashen waje ba. An hana maza ‘yan asalin kasar Ukraine da suka kai shekarun fada su fice daga kasar kwata-kwata.
Duk da haka, wasu 'yan Afirka - daga cikin dubban daruruwan mutane da ke kokarin ficewa daga Ukraine - suna zargin cewa ana nuna ma su wariyar launin fata, zargin da musantawa daga hukumomin Ukraine suka musanta, ya kuma sa Amurka da hukumomin kasa da kasa bayyana damuwa.
Augustine Akoi Kollie, dan kasar Laberiya da ke karatu a fannin aikin magani a birnin Ternopil da ke yammacin kasar Ukraine, ya ce ya gani da idonsa yadda ake nuna irin wannan wariyar lokacin da ya shafe dare yana jira ranar Asabar don tsallaka kan iyaka da ke kusa da Suceava, na kasar Romania.
Kollie ya shaidawa ga Muryar Amurka cewa, “Mutane su na tsayawa a kan layi suna rawar sanyi a cikin dogayen layi, suna rike da kaya da kananan yara, kuma "idan dan kasar Ukraine ya zo, dole ku matsa ku ba 'yan Ukraine damar zuwa gaba," Ko da yake hukumomi sun bukaci a fara ba mata da kananan yara, dama amma yace, an bar matan Afirka a baya,
Ya ce, "wariyar launin fata ne, domin idan ka ce kana daukar mata da yara, kana da dalibai 'yan kasashen waje a can mata ne, to me ya sa ba ka daukar su?"
Kollie ya kuma ga wani yanayin tashin hankali, inda daya daga cikin abokan tafiyarsa ya dauka hoton bidiyo yayin da suke jira a kan iyaka. Hotunan bidiyon da aka tura wa Muryar Amurka, ya nuna wani wurin da daddare da wasu mutane sanye da kayan aiki suna tunkude wani da Kollie ya ce ''dalibai na kasashen waje'' wadanda ke zaune a kasa kuma da kyar ake ganinsu a bayan wata motar da aka faka. Mutanen sun yi harbi a iska sau da dama.
Bayanin nasa ya yi daidai rahotannin da wasu kafafen yada labarai su ka yayata.
Wata likita ‘yar Najeriya ‘yar shekaru 24 ta shaida wa jaridar New York Times cewa ta shafe sama da kwanaki biyu a makale a kan iyakar Ukraine da Poland a garin Medyka na kasar Poland, inda masu gadi suka hana baki ‘yan kasashen waje su wuce lokacin da suke barin ‘yan kasar ta Ukraine
Likitar Chineye Mbagwu ta shaidawa jaridar The Times cewa, "Sun a marin su, su doke su kuma tura su karshen layin. Abin ya yi muni."
Maudu'in #AfricansinUkraine ya dade yana tashe a shafin Twitter, ana yayata faifan bidiyo na bakar fata da ke nuna kamar ana hana su shiga jirgin kasa ko kuma tada su tsaya da hana zu zama. Muryar Amurka ba ta iya tantance faifan bidiyo da kanta ba.
Wakilin Muryar Amurka da ya aiko da rahoto daga Ukraine ya ce hukumomi a can sun bai wa 'yan Ukraine fifiko wajen shiga motocin safa da jiragen kasa ke ficewa daga Ukraine, lamarin da ya sa ya zama da wahala baki su sami damar ficewa.
Wani jami’in Amurka, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce Amurka ta na bin diddigin labarin barin mutanen, kuma ya kasance “babban abin damuwa” duk da cewa ‘yan Najeriya sun kasance rukuni na biyu mafi girma na ‘yan kasashen waje da suka fice daga Ukraine ranar Talata.
"Ina tsammanin wannan ta zame masu wata babbar matsala, " in ji jami'in. "Kowa ya fuskanci wariya na tsawon kwanaki yayin da ake ba mata da yara fifiko."
Ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba, ya wallafa a shafinsa na twitter ranar Talata cewa: "Mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ya shafi 'yan kasar Ukraine da wadanda ba 'yan kasar ba ta hanyoyi da dama. 'Yan Afirka da ke neman ficewa abokanmu ne kuma suna bukatar dama ta bai daya don komawa kasashensu lafiya. gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen magance matsalar."
Rahotanni masu tada hankali
Kungiyar Tarayyar Afirka ta fitar da wata sanarwa ranar litinin tana mai cewa manyan jami'anta - shugaban Senegal na yanzu Macky Sall da shugaban hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat - "sun damu matuka da rahotannin da ke cewa an ki ba 'yan Afirka da ke bakin iyaka da Ukraine. 'yancin ketare iyaka zuwa tudun mun tsira"
Sanarwar ta ci gaba da cewa, "Rahotanni da ke nuna cewa an nuna wa 'yan Afirka wariya, da mu'amalar da ba ta dace ba, zai zama wani abu mai ban mamaki na wariyar launin fata da kuma keta dokokin kasa da kasa."
Kungiyar Red Cross ta kasa da kasa ba ta iya tabbatar da irin wadannan rahotannin ba, "amma suna da matukar tayar da hankali," in ji hukumar a cikin sakon imel da ta aike wa Muryar Amurka ranar Talata. "’Ikon neman mafaka da gudu zuwa tudun mun tsira hakki ga duk wanda rikici ya shafa. ICRC tana aiki da kuma daukar matakin taimakawa duk wanda fada ya shafa."
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi Allah wadai da duk wani yunkuri na hana 'yan Afirka ficewa daga Ukraine. "Muna sane da wadannan rahotannin kafafen yada labarai," in ji mai magana da yawun sashen a ranar Litinin. "Ba za a lamunci duk wani aiki na nuna wariyar launin fata, musamman a lokacin rikici ba."
Kakakin ya ce ma'aikatar tana "tattaunawa tare da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya a kasa don tabbatar da cewa an karbi kowane mutum da ya tsallaka zuwa kasashen da ke makwabtaka daidai da yadda aka karbi kowa, an kuma ba shi kariyar da ya ke bukata."
A halin da ake ciki, kungiyar ta AU ta yaba da kokarin da kasashe mambobinta da ofisoshin jakadanci a kasashe makwabta suke yi na karbar 'yan Afirka da iyalansu da ke kokarin ficewa daga Ukraine.
Jakadiyar Najeriya a Romania, Safiya Ahmad Nuhu, ta shaidawa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa sama da 'yan Najeriya 600 ne suka isa Bucharest "kuma akwai wasu da yawa a cikin motocin bas da ke fitowa daga wuraren shiga daban-daban."
Ta kara da cewa, "Hukumomin Romania sun taimaka matuka wajen hada kai, shiri da taimako." "Ba ma gwamnati kadai ba har ma da daidaikun mutane, kungiyoyi, jami'o'i, masu zaman kansu - duk sun taimaka sosai wajen ba da taimako."
Kollie, dalibin Laberiya, ya ce da zarar shi da abokansa biyu suka tsallaka zuwa Romania, an ba su barguna, abinci da yawa aka kuma dauke su zuwa garin Timisoara, inda suke raba dakin otal. Ya ce an shaida wa sabbin masu shigowa za su sami taimako da abinci da wurin kwana na kwanaki 30.
Ana sa ran karuwar ‘Yan Gudun Hijira
Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa, 'yan gudun hijira za su ci gaba da kwarara kan iyakokin Ukraine yayin da ta ke ci gaba da kai hari.
"Ba kasafai nake ganin irin wannan gudun hijirar na mutane ba," kuma adadin" yana karuwa kowacce sa'a tun ranar alhamis," in ji kwamishinan 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya Filippo Grandi, yayin da yake jawabi ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Litinin. "… A halin yanzu muna shirin samar da 'yan gudun hijira har miliyan 4 a cikin kwanaki da makonni masu zuwa. Irin wannan karuwar cikin sauri zai zama babban nauyi ga jihohi."
Grandi ya ce, karuwar da ake samu tana wakiltar kaura mafi girma a Turai tun bayan yakin Balkan a farkon shekarun 1990. Sama da mutane miliyan 2 ne suka tsere daga gidajensu, kamar yadda hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta a lokacin.
Grandi ya ce a halin da ake ciki yanzu, sama da mutane 280,000 ne suka nemi mafaka a Poland; a Hungary, 94,000; a Moldova, kusan 40,000; a Romania, 34,000; a Slovakia, 30,000 - da dubun dubatar wasu wurare a Turai. Grandi ya ce " wadansu mutane da dama" sun koma Tarayyar Rasha.
Hukumar Tarayyar Turai - reshen zartaswa na Tarayyar Turai - a farkon wannan makon ta tattauna batun neman kasashe membobin su ba da mafaka na wucin gadi ga 'yan Ukraine har na tsawon shekaru uku, in ji jaridar New York Times.
Mazauna kasar Ukraine, wadanda a ranar Litinin din da ta gabata suka nemi zama mamba a kungiyar ta EU, a halin yanzu za su iya zama na tsawon kwanaki 90 da kuma tafiya ba tare da biza ba a cikin kasashen kungiyar.
Da Muryar Amurka ta tambaye ta game da manufofin EU da tanade-tanade ga 'yan gudun hijirar Yukren da sauran 'yan gudun hijira, Hukumar Tarayyar Turai ta fada a cikin imel a ranar Talata cewa " nan ba da jimawa ba za ta ba da shawarar samar da Dokar Kariya ta wucin gadi don ba da taimako cikin sauri da inganci ga mutanen da ke tserewa yakin Ukraine. Hukumar a shirye take ta tallafa wa kasashe mambobinta da ke ba da mafaka ga mutanen da ke tserewa daga Ukraine kuma tana aiki kan wani shirin ko-ta-kwana don mayar da martani ga cin zarafin da Rasha ke yi, wanda ya hada da kare al'ummar Ukraine ... muna nazarin dukan matakan da za a iya dauka da za su taimaka wa Jihohi karbar masu shigowa cikin sauri da inganci, ba za mu iya yin karin bayani ba har sai mun gabatar da shawararmu."
Dangane da yadda ake cin zarafin wasu tsiraru, hukumar ta ce: " Ya kamata a ba da damar shiga EU ga duk mutanen da suke bukata, ba tare da la'akari da kasarsu, kabila, ko launin fatarsu ba, wadanda ke gudun tashin hankali a Ukraine."
Wadanda su ka bada gudummuwa a rubuta rahoton: Shugaban ofishin Muryar Amurka na gabashin Turai Myroslava Gongadze, Grace Alheri Abdu, Sashen Hausa, Muryar Amurka, Ignatius Annor, Sashen Turanci na Muryar Amurka, Wakilin da ke dauko rahotannin harkokin tsaro na Kasa Jeff Seldin, Betty Ayoub, da Carol Guensburg Yankin Afirka