Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Za a Magance Matsalar Tsaro a Hanyar Abuja-Kaduna – Sanata Shehu Sani


Sanata Shehu Sani
Sanata Shehu Sani

A Najeriya, ana ci gaba da laluben hanyoyin da za a iya magance matsalar masu garkuwa da mutane akan hanyar Abuja zuwa Kaduna bayan wani mummunan harin da ‘yan bindiga suka kai a baya-bayan nan.

Mai fafutukar kare hakkin bil adama Sanata Shehu Sani, ya ba hukumomin Najeriya shawara kan yadda za a magance matsalar garkuwa da mutane da ‘yan bindiga ke yi akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

A cewar Sanata Sani, hanya daya da za iya magance wannan matsala ita ce a dauki matasan kauyukan da ke kan hanyar a aikin dan sanda da na hukumar tsaron al’uma ta Civil Defence a kuma tura su yankunan domin su samar da tsaro.

“Akwai kauyyuka 37 akan wannan hanya. A dauki matasan wadannan kauyuka a aikin dan sanda sai a tura su aiki a wadannan kauyuka don su rika kare hanya su kuma tunkari masu garkuwa da mutanen, domin sun san yankin sosai.” Sani ya fada a shafinsa na Twitter.

Rahotanni sun ce a farkon makon nan ‘yan bindigar suka datse hanyar ta Abuja zuwa Kaduna da tsakar rana suka yi awon gaba da mutane da dama cikin har da daliban Jami’ar Ahmadu Bello da ke kan hanyarsu ta zuwa Legas.

Sanata Sani ya kuma bukaci da a yi garanbawul ga runduna ta musamman da aka kafa don yaki da ‘yan bindigar ta Puff Adder idan har ana son a magance wannan matsala.

Sakon Twitter na Sani ya kara da cewa, “a wannan fannin (na tsaro) ake bukatar hankulan gwamnonin arewacin Najeriya.”

A yau Talata shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yake jagorantar taron kwamitin tsaron kasa a fadarsa inda taron zai fi mayar da hanakli kan “kan al’amurna da suka faru a akan hanyar ta Abuja zuwa Kaduna da sauran matsalolin tsaro a sassan kasar,” a cewar wani sakon Twitter da Bashir Ahmad da ke ba Buhari shawara kan harkokin kafafen sada zumunta ya wallafa a yau.

Matsalar tsaro akan hanyar ta Abuja, babban birnin kasar zuwa Kaduna da ke makwabtaka ta haifar da asarar rayukan daruruwan mutane da kudaden fansa da ake biya domin kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su.

Baya ga matsalar garkuwa da mutane a wannan hanya, jihohin Katsina, Zamfara da Sokoto su ma suna fama da matsalar hare-hare 'yan bindiga da ta yada da yin garkuwa da mutane, sace dabbobi da cin zarafin mata.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG