Masu sa ido a zaben kasar Togo sun ce mutane masu yin zabe sun fito da kimanin kaso arba'in na masu kada kuri’ar. Faure Gnassingbe ya dare karagar mulki a shekarar 2005 bayan mutuwar mahaifinsa Gnassingbe Eyadema wanda ya mulki kasar tsawon shekaru talatin da takwas.
Shima Jean-Pierre Fabre da ya taba fitowa takara a zaben da ya gabata ana sa ran zai zo na biyu a zaben tashin farko na zaben shugaban kasa.
Masu rajin kare hakki sun soki Togo da amfani da karfin tuwo akan masu zanga-zanga. Daruruwan masu sa ido sun sauka a Togo don ganewa idanunsu yadda zata kaya a zaben da ake sa ran masu kada kuri’a Miliyan 3 da rabi ne da zasu wakilcin rabin yawan jama’ar kasar.