Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arangamar 'Yan Sanda Da Jama'ar Burundi


'Arangamar Yan Sanda
'Arangamar Yan Sanda

A yau lahadi ‘yan sanda a babban birnin Burundi wato Bujunbura, sun yi karon batta da masu zanga-zangar kin amincewa da tazarce karo na 3 da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ke neman yi.

‘Yan sandan sun ta harba borkonon tsohuwa cikin gungun jama’ar don hana su kutsawa cikin tsakiyar birnin. Shedu sun ce sun ga an raunata mutane da dama wasu kuma an kakkamasu.

Gwamnatin kasar dai ta haramta ko wace irin zanga-zanga game da hukuncin da jam’iyyar CNDD-FDD mai mulki ta yanke na tsayar da Nkurunziza a matsayin dan takarar shugabancin kasar a karo na uku.

Amincewa da shi din ta biyo bayan wani taron yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya ne da kuma alkinta kundin tsarin mulkin kasar. Tsarin siyasa a Burindi ya faro ne tun a taron yarjejeniyar nan mai lakabin ARUSHA a shekarar 2000.

Wannan ne ya kawo karshen mugun yakin basasar kabilar Hutu da Tutsi da ya hallaka mutane sama da dubu dari uku. Sai dai a yarjejeniyar ba’a yarda wani shugab yayi wa’adin mulkin da ya wuce sau biyu ba.

Kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 2005 yace dole sai wanda za’a zaba ya samu mafi yawan kuri’u. ‘Yan majalisar kasar dai ne suka fara zabar Nkunziza a matsayin shigaban kasa inda daga baya magoya bayansa suka nuna cancantarsa ta sake tsayawa karo na biyu a milkin kasdar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG