Kamar yadda guguwar canji ke kadawa a Najeriya, wasu fitattun ‘yan jam’iyar adawa ta PDP sun yi bayanin cewar da sa hannun su jam’iyar tasu ta sha kaye haka kuma da sa hannun su jam’iyar APC wadda dan takarar ta ya lashe babban zaben gwamnatin kasar.
Alhaji Aliyu Mustapha Sokoto yayi hira da daya daga cikin ‘yayan jam’iyar PDP wadda ta sha kaye a babban zaben da ya gabata, kuma daya daga cikin manyan dattawan da ake mutuntawa a fadin kasar kuma tsohon minister wato Ambasada Fidelis Tapgun, yayi Karin bayanin yadda hakan ta faru da kuma dalilan da suka karkatar da hankulan su dan yin hakan.
“Gaskiya ne mun taimaki jam’iyar APC ta janar Muhammadu Buhari mai jiran gado wajan lashe babbabn zaben kasa da akayi, kuma ba abin da mukayi a boye bane domin mun ja kunnen shugabannin jam’iyar mu ta PDP akan abubuwa da dama wadanda ka iya sa jam’iyar ta fadi zabe amma sukayi abubuwan da suka ga dama kawai”.
A cikin abubuwan da suka fi bata masu rai a cewar shi sun hada da sayen tikitin shiga takara ba tare da la’akari da wasu abubuwa da dam aba. A cewar shi, dole sai wadanda suka ga dama kadai ke iya samun tikitin kuma haka ya faru a duk fadin Najeriya.
“bazamu bari irin wasu halaye marasa nagari na gwamnatin jahar su cigaba ba, shiya sa daukacin jama’ar Filato suka fito kwan su da kwarkwatar su wajan zabe. Domin idan ba hakan mukayi ba to lallai kowa zai zama tamkar bawa Kenan a jahar filato”.
A matsayin tsohon gwamnan jahar filato, inji Mr Tapgun ya kara da cewar “ni na kawo shi domin shi kadai bazai iya cin zabe ba, kuma koda na kawo shi jama’a da dama sun ta fadi kamar da wasa cewar ka kawo mana kayan da bashi da inganci, kuma yana hawa sai kawai ya zama dodo ba mai Magana da shi kuma”.