Rahotanni daga jamhuriyar Nijar sun bayyana cewar matar tsohon shugaban kasar marigayi Ba’are mai nasara ta garzaya kotun majalisar hadin kan kasashen Afirka wadda aka sani da ECOWAS da ke babban birnin Najeriya Abuja domin neman a bi bata hakki.
Kamar yadd Alhaji Hamisu Kalah ya bayyana a hirar su da Mani Chaibu, wannan mataki da ta dauka abin da an dade ana tsammanin za ayi ne dan haka ba wani abin mamaki a ciki.
Alhaji Hamisu Kalah ya kara da cewar “hatta wadanda suka aikata wannan aika aika ko da sun tafi lahira sun san cewar lallai lokacin na zuwa da matar tsohon shugaban zata nemi a bi mata hakkin ta, kuma matakin da ta dauka hatta masu mulki zasu ji dadin hakan saboda kada hakan ta faru da su watarana”.
Ya kuma kara da cewar a kwankin baya sunyi wani taron ‘yan jarida kuma sunyi Allah wadai da duk wanda zai sa karfin bindiga ya kashe dan adam ko talaka ko mai mulki, dan haka neman hakkin da ta je nema abinda ya kamata ne.
Matar Tsohon shugaban dai ta kai karar ne tare da goyon bayan mahukuntan kasar kuma a cewar shi, lallai akwai alamun samun nasara ga wannan yunkurin da ta yi, kuma babu wata matsala da hakan zai haifar a duk fadin kasar ta Nijar.