Wata kungiyar kare hakkin bil’adama mai shelkwata a Birtaniya da ke lura da yanayin yakin Syria, sun ce akalla an harba makamai hudu da suka ragargaji birnin, wanda shi ne ya ragewa gwamnati da take iko da shi a yankin Idlib.
Hakan na faruwa ne bayan da ‘yan tawaye suka kwace ikon babban birinin yankin Idlib wata guda da ya wuce.
Kwace garin Jisr al-Shughour mai kimanin mutane dubu 50 na daga cikin jerin biranen da Damascus ta rasa a arewa da Kudancin yankunan Syria.
Babu takamaiman rahoton wadanda suka mutu a harin na yau, amma kungiyar kare ‘yancin dan adam din ta ce akalla mutane 27 suka mutu a harin jiya asabar, ciki har da ‘yan tawayen.
Kafar yada labaran gwamnati ta ce sun fito da dakarunsu wajen Jisr al-Shughour domin gujewa ci gaba da raunata fararen hula.