Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Neman Wata Likita ‘Yar Kasar Poland Da Aka Yi Garkuwa Da Ita Daga Asibiti A Kasar Chadi


Wani asibiti a N'Djamena, Chad
Wani asibiti a N'Djamena, Chad

Ana ci gaba da neman wata likita ‘yar kasar Poland da aka yi garkuwa da ita a kudancin kasar Chadi, kamar yadda jami'ai da kafafen yada labarai a kasar Poland suka ruwaito yau Litinin.

WASHINGTON, D. C. - Matar tana aikin sa kai ne a asibitin Saint-Michel da ke da nisan kilomita dari daga babban birnin kasar ta Afirka ta Tsakiya, lokacin da maharan da suka yi ikirarin cewa basu da lafiya ne, amma sai suka sace ta tare da wata likitan kasar Mexico, kamar yadda Polsat News, wani gidan yada labarai mai zaman kansa na kasar Poland ya ruwaito.

Dr. Carlos Solgado ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Associated Press ta wayar tarho cewa ya tsere ne a lokacin da wani rikici ya barke tsakanin masu garkuwa da mutanen da jami'an tsaron Chadi, yayin da aka sace matar 'yar Poland.

Ya ce harin ya faru ne da safiyar Juma’a lokacin da wasu mutane hudu dauke da makamai a kan babura biyu suka shigo asibitin. Solgado ya ce masu garkuwa da mutanen sun shaida musu cewa kudi kawai suke so kuma ba su da niyyar kashe su.

Ana dai yawan yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a yankin Tanjile, inda aka yi garkuwa da su.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Poland ta ce sojojin Chadi da na Faransa na neman matar kuma jami'an diflomasiyya da na ofishin jakadancin Poland suna hulda da hukumomin yankin da dangin matar.

A cikin shekarar 2021, an yi garkuwa da wani ‘dan Faransa daga gabashin kasar amma an same shi da rai bayan kwana biyu.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG