Galibin kananan hukumomin dai suna iyaka da jihohin Kaduna, Zamfara da Kebbi da kuma Abuja, fadar gwamnatin Najeriya.
Jihar Neja dai na daya daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da ta fuskanci matsalar hare-haren 'yan bindiga da garkuwa da mutane tun daga shekara ta 2017 zuwa wannan lokaci.
Koda yake dai izuwa lokacin hada wannan rahoto bayanan da Muryar Amurka ta samu, ya nuna an samu saukin kai hare-haren da wadanan 'yan fashin daji ke kaiwa a wadanan kananan hukumomi.
Hakan ne ya yi sanadiyar taruwar masu ruwa da tsaki akan sha’anin tsaro domin ci gaba da tattaunawa kan shawo kan matsalar rashin tsaro da ya shafi sassa daban daban na yankin Arewacin Nigeria.
Hakazalika, a wani babban taron da aka gudanar a karshen makon nan da ya gabata a masarautar Kontagora, yankin da ya sha fama da matsalar 'yan bindigar, mahalarta taron sun tattauna akan sahihan hanyoyin bi da za su taimaka wajen shawo kan lamarin.
Shugaban Karamar Hukumar Mariga, dake cikin mahalarta wannan taro, yayi bayanin yadda karamar hukumarsa ke ci gaba da fuskantar matsalar 'yan fashin dajin.
Farfesa Bashir Danlami, Sarkin Daji na Jamiyar Ibrahim Babangida dake Lapai, na daya daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai a taron, in da yace dole ne sai shugabanni sun kula da matasa sannan a samu saukin wannan matsala
Duk da Haske da ake gani wajen samun saukin lamarin dai, masana suka ce dole aci gaba da neman hanyoyin da zai sa saukin ya dore kamar yadda wakilin gwamnan jihar Neja a taron kuma Shugaban Karamar HUkumar Kontagora, Alh. Shehu s Pawa ya bayyana.
Ga cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Dandalin Mu Tattauna