WASHINGTON, D. C. - Wasu gungun ‘yan bindiga ne suka yi garkuwa da mutanen kauyuka da matafiya da dalibai domin karbar kudin fansa, yayin da kasar da ta fi kowacce yawan al’umma a Afirka ke fama da matsalar rashin tsaro, wanda kuma ya hada da matsalar ‘yan tada kayar baya na Islama a yankin arewa maso gabas.
A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar Ekiti ta fitar ta ce an yi garkuwa da daliban ne da malaman a lokacin da suke dawowa daga balaguron gida a daren ranar Litinin. Haka zalika an dauke duk da direban bas din makarantar.
Sanarwar ta kara da cewa, jami'an tsaro a jihar na kan bin sawun wadanda suka yi garkuwa da su.
Babu wanda ya dauki alhakin ko ya nemi kudin fansa.
Shugaba Bola Tinubu, wanda ya mayar da hankali wajen farfado da tattalin arzikin kasar da ya tabarbare, na fuskantar karin bincike kan yadda aka yi ta yin garkuwa da mutane a fadin Najeriya, ciki har da a wajen Abuja babban birnin kasar cikin wannan wata.
Jagoran ‘yan adawa Atiku Abubakar a ranar Talatar ya zargi Tinubu da “yin wasa a lokacin da Najeriya ke nutsewa cikin rashin tsaro,” yana mai nuni da ziyarar da shugaban ya kai kasar Faransa na kashin kansa na tsawon mako guda.
Dandalin Mu Tattauna