Manufar taron shi ne horas da 'yan siyasa akan yadda zasu cike takardun neman shiga zaben shekarar 2016 ba tare da tabka kuskure ba.
Maryamu Katambe mataimakiyar shugaban hukumar zabe ta yi karin haske kan lamarin. Tace a takardun wancan zabe da 'yan siyasa suka cika an zubar da dama cikinsu saboda kurakurae da suka yi. Tace gujewa sake aukuwar abun da ya faru baya ya sa suka shirya wannan taron. Tace basa son a sake tabka kurakurai irin na shekarar 2010.
A nasa bangaren shugaban hukumar rayar da dimokradiya ya bayyana irin nauyin da ya rataya a wuyan kowane bangare na ganin cewa an shirya zabuka nagari a shekarar 2016 a kasar ta Nijar. Wannan nauyin ba wai gwamnati ko hukumar zabe ba ne kawai ya rataya a wuyansu ba.Ko su ma 'yan siyasa nauyin ya rataya akansu domin ganin an shirya zabuka na gari ko suna bangaren gwamnati ko adawa. Saboda haka akwai mahimmanci 'yan siyasa su samu horo. Yace wannan shi ne burin da taron yake son ya cimma.
Abdu Muhammed Yarima daya daga cikin 'yan siyasa ya godewa Allah da hukumomin da suka shirya taron saboda zai taimaka ainun wurin rage kurakurai.
To saidai an yi korafin karancin mata a taron lamarin da Maryam Katambe tace ba zasu amince da shi ba saboda doka ta basu wani kaso a gwamnati.
Ga karin bayani.