Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Sun Yi Zanga Zanga a Nijar


Lokacin Matasa suna zangar zangar Chalrie
Lokacin Matasa suna zangar zangar Chalrie

Matasa a tsibirin Gobir da ke Jihar Maradi, sun yi ta kone-kone bayan da suka ji jita-jitar za a sanya shingayen binciken ‘yan sanda tsakanin birnin Maradi da tsibirin.

Rahotanni sun ce matasan sun yi kaca-kaca da ma’aikata da kuma gidan Magajin Garin.

“Saboda an saka gate tsakanin Tsbiri da Maradi, shi ne ya sa matasan suka ce sub a su yarda ba, matasan sun yi maci har zuwa gidan sarki inda suka yi ta jifa.” In ji wani wanda ya shaida lamarin.

Bayanai sun kara nuni da cewa matasan sun datse wasu hanyoyin motoci, lamarin da ya hana zirga zirgan ababan hawa.

Sai dai akwai rahotanni da ke cewa sai da ‘yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye kafin a tarwatsa su.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG