Shugaban kasar Nijar ya kaddamar da hanyar mai tsawon kilomita 42 da ta tashi daga Damagaran zuwa Musari ne.
Gwamnatin kasar tare da tallafin Tarayyar Turai suka dauki nauyin gina hanyar mai kwalta.Hanyar ta rage lokacin dake daukan mutane su yi balaguro daga Damagaran zuwa Musari daga awa uku zuwa mintuna 45 kacal.
Yayin da yake kaddamar da hanyar shugaban Nijar Mahamadou Issoufou yace ya godewa Allah da ya gwada masu ranar cika alkawalin da suka dauka. Ba wannan alkawalin ba ne kadai suka cika. Akwai wasu da yawa da gwamnatinsa ta cika.
Shugaban yace gwamnatinsa ta dauki alkawura takwas kuma cikin shekaru biyar ta cikasu. Ta cika alkawarin samarda kwanciyar hankali.Ta inganta dimukradiya.Ta gyara hanyoyin mota da sauransu. Ta farfado da ilimi a kasar. Ta kula da lafiyar jama'a da ba jama'a ruwan sha. Ta ba matasan Nijar ayyukan yi.
Ba shakka hanyar ta kawo sauki ga matafiya domin yanzu maimakon yin awa uku a hanya zasu yi tafiyar cikin mintuna 45 kawai. Hanyar zata kawo ragowa ga kudin sufuri da kuma rage tsadar kaya musamman kayan gona.
Jama'ar yankin sun yi murna da samun wannan sabuwar hanya suna kuma fata 'yan kasuwa zasu rage kudin kayansu domin hanya ta samu.
Ga karin bayani.