Shugabannin masu zanga zanga a kasar Masar sun yi kira da a gudanar da yajin aikin gama gari yau Talata a wani sabon yunkurin matsawa shugaba Hosni Mubarak lamba ya mika mulki bayan gwamnati ta yi kokarin cin moriyar wannan yunkurin ta wajen yiwa ma’aikatan gwamnati miliyan shida karin kashi goma sha biyar bisa dari na albashi . Masu zanga zangar kin jinin gwamnati sun killace wani sansani a dandalin Tahrir Square suka kuma lashi takobin ci gaba da zama a wurin har sai Mr. Mubarak ya sauka daga karagar mulkin da ya rike na tsawon shekaru talatin. Suna kyautata zaton wadansu mutane da dama zasu shiga sahun masu zanga zangar yau talata. jaridar New York Times ta laburta cewa masu zanga zangar suna kuma tunanin shirya irin wannan zanga zangar a sauran manyan biranen kasar Masar da kuma ketare doka ta wajen yiwa shelkwatar talabijin ta kasar kawanya, wadda masu zanga zangar suke kyama sabili da sun dauka baya tare da su
Shugabannin masu zanga zanga a kasar Masar sun yi kira da a gudanar da yajin aikin gama gari yau Talata a wani sabon yunkurin matsawa shugaba Hosni Mubarak lamba ya mika mulki