Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Masar Sun Hana Cin Zarafin 'yan Zanga-Zanga


Mataimakin shugaban kasar Masar Omar Suleiman yake ganawa da wakilan masu zanga zanga.
Mataimakin shugaban kasar Masar Omar Suleiman yake ganawa da wakilan masu zanga zanga.

Frayin Ministan Masar yace hukumomi a Alkhira da kuma wasu birane inda masu zanga zanga suke ci gaba da bori,an bada umurni kada a ci zarafinsu, kada a tsare ‘yan gwagwarmaya ko ‘yan jarida.

Frayin Ministan Masar yace hukumomi a Alkhira da kuma wasu birane inda masu zanga zanga suke ci gaba da bori,an bada umurni kada a ci zarafinsu, kada a tsare ‘yan gwagwarmaya ko ‘yan jarida.

Jami’an Amurka sunce sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton a zantawa da ta yi da PM Ahmed Shafiq ta nemi gwamnati ta tsai da duk wata muzgunawa ga ‘yan gwagwarmaya da ‘yan jarida da ma wasu jama’a dake kungiyoyi masu zaman kansu.

A yammacin Asabar ce Clinto ta yimagana da PM,kuma PM ya tabbatar jiya lahadi cewa za’a daina tsare mutane.

Mr. Shafiq ya gayawa ‘yan jarida daga tashar talabijin ta CNN cewa an umurci jami’an gwamnati su daina damun ‘yan gwagwarmayar kare hakkin bil’adama da ‘yan jarida a wurare da ake zanga zanga nuna kyamar gwamnati.Yace an haramata irin wadan nan kame kamen baki daya.

Ahalin yanzu kuma mataimakin shugaban kasar ya yi shawarwari da ba’a taba irinta ba kan sauye sauye ga harkokin siyasa da jerin rassan ‘yan hamayya ciki harda haramtacciyar jam’iyyar Muslim Brotherhood.Yanzu kusan mako biyu da fara zanga zangar neman ganin shugaban kasa Hosni Mubarak ya yimurabus nan da nan, har yanzu ana shirya gangamin msu hamayya d ashugabancinsa.

Duk da sassaucin da mataimakin shugaban kasa Omar Suleiman ya gabatar a garambawulga harkokin siyasar kasar,’yan hamayya sun dage cewa suna bukatar ganin shugaba Hosni Mubarak ya yi murabus.

Ahalin yanzu kuma,sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tace Amurka zata zuba ido ganin yanzu an shiga shawarwari da masu da’awar Islama da gwamnatin Masar,gameda tarzoma da ake ci gaba da yi a gidan.

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG