Masu zanga zangar kin jinin gwamnati sun gudanar da zanga zanga mafi girma da suka taba yi cikin makonni biyu, suna kara jaddada bukatarsu ta ganin shugaba Hosni Mubarak ya sauka daga karagar mulki ba tare da bata lokaci ba, yayinda suka bayyana kin amincewa da matakan da gwamnati ta dauka na yin garambawul.
Jami’in kamfanin bincike na yanar gizon nan google, da aka saki, wael Ghonin, ya tsima masu zanga zangar da mara masu baya da ya yi a karon farko bayan sakinshi ranar Litinin, daga kulleshi da aka yi na tsawon kwanaki goma sha biyu.Ghonim ya shaidawa masu zanga zangar cewa, “ba zamu yi watsi da bukatarmu ta neman ganin bayan wannan gwamnatin ba.”
Mutane da dama sun shiga sahun masu zanga zangar a Tahrir Square karon farko jiya Talata, da suka hada da dubban manyan malaman jami’oi da lauyoyi. An kuma yi zanga zanga a birnin Alexandria da sauran birane.
Mataimakin shugaban kasar Omar Suleiman ya bayyana jiya Talata cewa, Mr.Mubarak ya bada izinin kafa kwamitoci dabam dabam da zasu yi garambawul a kundin tsarin mulkin kasar da kuma sa ido wajen aiwatar da shi.
Za a yi garambawul din ne da nufin yin sassauci a damar shugaban kasa ta tsayawa takara da kuma kayade wa’adin shugabanci, wata muhimmiyar bukata da ‘yan hamayyar kasar Masar suka gabatar.