Shaidu a Ivory Coast sun ce gobara ta tashi a wani gini ofisoshin baitulmalin kasar jiya Talata.Rahotanni daga birnin Abidjan na nuni da cewa, wuta ta rika ci a, a kalla hawa uku na ginin benen kafin masu kashe gobara su shawo kanta.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambaci ta bakin majiyoyin rundunar soji cewa, babu wanda yaji rauni a gobarar. Babu tabbacin abinda ya haddasa gobarar, ko kuma idan tana da wata alaka da rudamin siyasa da ake fama da shi a kasar.
Shugaba Laurent Gbagbo mai ci yanzu yaki mika mulki ga abokin hamayyarsa Alassane Quattara, wanda akasarin kasashe suka hakikanta cewa shine ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar cikin watan Nuwamba.Shugabannin biyu suna ta kokarin samun karfin iko kan kudin kasar.
A wata sabuwa kuma, jiya Talata shugaban kungiyar ECOWAS ya kushewa Afrika ta Kudu domin tura jirgin yakinta ruwayen Ivory Coast. James Victor Gbeho yace jiragen yakin zasu kara dagula lamur ne kawai.