Shugaban Masar Hosni Mubarak ya bijirewa bukatar dubun dubatan masu zanga zanga da ke kiran ya yi murabus yanzu,bayan shekaru 30 yana mulkin kasar.
A jawabi da ya yi wa al’umar kasar ta atalabijin a daren jiya, Mr.Mubarak ya dai fadi cewa zai mika wasu daga cikin ikonsa na shugaban kasa ga mataimakinsa.
Shugaban yace zai miko ikon harkokin yau da kullum ga mataimakin shugaban kasa Umar Suleiman.Jami’an Masar suka ce shugaba Hosni Mubarak zai ci gaba da rike ikon rushe majalisa da gwamnati,da kuma kaskwarima ga tsarin mulkin kasar.
A cikin jawabin, Mr. Mubarak yace yana magana ne ga ‘yayansa maza da mata ma’ana al’umar kasar, yana mai aibunta ‘yan kasashen waje dake neman katsa landan cikin harkokinn Masar.
A dandali da masu zanga zanga suka hallara suna jiran suji shugaban zai sauka,nan da nan murna ta koma ciki. Suka fusata suna irr,kuma suka fara kira da babban muriya “tilas ka tafi”. Suna nuna takalmansu,alamar reni a al’adar larabawa.
Wasu masu zanga zanga kamar dubu biyu suka yi maci zuwa tashar talabijin da Radiyo ta kasar dake da 'yar tazara daga sansanin zanga zangar. Wasu daruruwa kuma suka hallara a harabar gidan shugaban kasa dake gundumar Heliopolis,kamar kilomita 8 daga tsakiyar birnin Alkahira.
Masu shirya zanga zanga sun yi alkawarin yau jumma’a ce zasu hada gangamain daba’a taba ganin irinta ba a kasar.
Jiya Alhamis shugaban Amurka Barack Obama yace an gayawa ‘yan kasar Masar,cewa akwai shirin mika mulki,amma abinda ba sani ba shine ko canjin nan take ne,mai ma’ana kuma ko ya wadatar.