Duk da ruwan saman da aka rika zubawa kamar da bakin kwarya, daruruwan mutane sun hallara a dandalin Times Square na birnin New York domin su nuna rashin jin dadinsu da zaman sauraron shaidar da ake shirin gudanarwa a majalisar wakilai game da hatsarin tsageranci a tsakanin Musulmin Amurka.
Masu zanga-zangar, wadanda suka hada da shugabannin addinai dabam-dabam, sun yi wannan gangami domin kare Musulmin Amurka daga abinda suka kira matakan nuna kyamar Musulmi.
Tun fari jiya lahadi, shugaban Kwamitin harkokin Tsaron Cikin Gida a Majalisar wakilan tarayya ta Amurka, Peter King, ya kare shirinsa na kiran zaman sauraron shaida a kan wannan batu mai sosa zuciya.
King, dan jam'iyyar Republican daga Jihar New York, ya fada a wani shirin gidan telebijin na CNN cewa zaman sauraron shaidar ya dace saboda Amurkawa masu koyi da al-Qa'ida su na yin barazanar tsaro ga kasa.
Amma Musulmin farko da aka taba zaba a majalisar wakilan tarayya ta Amurka, Keith Ellison, dan jam'iyyar Democrat daga Jihar Minnesota, ya fada cikin wannan shiri cewa ya damu da kokarin da ake yi na ware addini guda ta 'yan tsiraru a kasar nan domin gudanar da irin wannan binciken.
An shirya gudanar da wannan zaman sauraron shaida a ranar alhamis.