Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Falasdinawa Na Rububin Ficewa Daga Arewacin Gaza


Wasu Falasdinawa yayin da suke ficewa daga Gaza
Wasu Falasdinawa yayin da suke ficewa daga Gaza

Hamas ta yi watsi da gargadin na Isra’ila wanda ta kwatanta a matsayin farfaganda.

Falasdinawa da ke zaune a arewacin yankin Zirin Gaza, na fadi-tashin ficewa daga yankin yayin da wa’adin sa’a 24 da Isra’ila ta ba su su fice ke karatowa.

Isra’ila ta ba fararen hula da ke arewacin yankin umarnin su fice yayin da ake fargabar tana shirin kutsawa cikin Gaza don fafatawa da mayakan Hamas.

Akalla fararen hula sama da miliyan daya ake tunanin za su fice domin komawa kudancin yankin.

Hamas ta yi watsi da gargadin na Isra’ila wanda ta kira farfaganda.

A ranar Juma’a dakarun tsaron Isra’ila na IDF suka ba da tabbacin cewa sun sanar da mazauna birnin Gaza kan su fice “domin kare lafiyarsu.”

“Za ku iya dawowa yankin na Gaza idan muka fitar da sanarwa hakan.” Kakakin IDF Laftanar Kanar Jonathan Conricus ya ce.

Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito kungiyar ta Hamas tana kira ga al’umar yankin “da su zauna a gidajensu su kuma tsaya-tsayin daka saboda sanarwar ta farfaganda ce.”

Jakadan Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya, Riyad Mansour, ya fadawa manema labarai a ranar Juma’a cewa, umarnin da Isra’ila ta bayar na ficewa, daidai yake da “kisan kare dangi” na daruruwan dubban Falasdinawa wadanda babu inda za su iya zuwa.

Isra’ila ta jibge dakarunta dubu 300 a kusa da iyakarta da Gaza, amma kuma ta ce ba ta yanke shawarar kan ko za ta kutsa cikin yankin ba.

Sai dai ta ci gaba da yin luguden wuta a Gaza, inda ta ce ba za ta kakkauta ba har sai Hamas ta saki Yahudwa 150 da ta kama.

A ranar Asabar din da ta gabata, mayakan Hamas suka kai wani harin ba-zata a kudancin Isra’ila lamarin da ya sanadin mutuwar daruruwan Yahudawa.

A hare-hare martanin da ta kai, Isra’ila ita ma ta halaka daruruwan Falasdinawa tare da katse hanyoyin wutar lantarki, ruwa da man fetur.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG