:
Wata kotun Amurka ta daure wata ‘yar wasan kwai-kwayo wacce take fita a wasu shirye shiryen talabijin har da wani silima mai suna “The Blind Side, saboda ta aikewa shugaban Amurka Brack Obama da kuma tsohon magajin garin New York Michael Bloomberg wasika da aka sakawa sinadarai masu guba da ake kira “Ricin” da turanci.
Jiya talata wani alkalin kotun tarayya ya yankewa Shannon Guess Richardson daga jihar Texas daurin shekaru 18 a fursina abunda doka ta tanadar, a karkashin wata yarjejeniyar da ta kulla da masu gabatar da kara, saboda laifin mallaka ko sarrafa sinadarai masu guba.
A cikin watan Mayu na shekarar 2013 ne Richardson ta aikawa shugaba Obama da tsohon magajin garin New York Michael Bloomberg wasikun. Amma sai ta tafi gun ‘Yansanda tana zargin mijinta da wannan laifi. Tuni mijin ya shigar da takardun neman rabuwa da ita a gaban kotu.
Saboda bayanai masu karo da juna da take bayarwa ya sa masu bincke suka hakikance cewa itace dai ta aike da wasikun. Wata daya bayan haka ne aka kama ta.