Isra’ila ta kaddamar da hare hare masu yawan gaske kan zirin Gaza jiya talata, yayinda take dab da kaddamar hari ta kasa kan zirin-gazar da zummar hana falasdinawa harba rokoki kan Isra’ila.
Ministan tsaron Isra’ila Moshe Ya’alon yace a shirye kasar Bani Yahudun take ta kaddamar hari kan Hamas a Gaza “wanda ba zata kammala shi cikin ‘yan kwanaki ba”.
Majalisar tsaron kasar ta baiwa rundunar mayakan kasar izinin ta kuma umarci sojojin kasar na wucin gadi su dubu 40 suyi damara su hadu da takwarorinsu dubu daya da dari biyar da tuni suka gabato bakin aiki.
Rundunar sojojin Isra’ila tace hare hare da take kaiwa da jiragen yaki a bangaren wani matakin kare kanta ya auna wurare daban daban fiye da dari ciki harda da gidajen kwana da wuraren da ake harba rokoki. Jami’an yankin Falasdinu sun ce hare haren na isra’ila ya kashe akalla mutane 19 ciki harda yara uku.
A Washington kakakin fadar white House Josh Earnest yayi Allah wadai da hare haren rokoki da Hamas take kaiwa kan Isra’ila ya kuma ce Isra’ila tana da ‘yancin kare kanta.