Shugaba Barack Obama na Amirka yace samun kwanciyar hankali a duniya nan gaba, zai dogara ne ga ci gaba da dogora da kai na kasashen Afirka.
Jiya Litinin shugaba Obama yayi wannan furuci a nan birnin Washington, D.C. lokacinda yake yiwa matasa dari biyar da suke halarta bitan da ake yiwa shugabanin Afrika matasa.
Matasan suna halartar horon mako guda akan iya shugabanci.
Ana bada horon ne, kafin ayi taron kolin kimamin shugabanin kasashen Afrika hamsin a makon gobe idan Allah ya kaimu anan birnin Washington, D.C.
A jawabin daya gabatar shugaba Obama ya bukaci mahalarta bitan da su kare yancin mata. Haka kuma ya yabawa nasarorin da mahalarta bitan suka samu a kasashen su.
Mahalartan bitan sun buge da yin tafi, a lokacinda shugaba Obama yace za'a canjawa bitan suna domin mutunta gwazon yaki da mulkin wariya, tsohon shugaban Afrika ta kudu marigayi Nelson Mandela.