An kawo gawar marigayi babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, zuwa Abuja a safiyar Alhamis, inda ake shirin gudanar da jana’izarsa a ranar Juma’a.
Akwatin gawar Lagbaja, wanda aka lullube da tutar Najeriya, ya bar Legas tare da rakiyar manyan hafsoshin soji, kuma jirgin saman sojoji ya sauke gawarsa a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe Abuja da misalin karfe 12:16 na rana.
Za a fara taron addu’o’in tuna marigayin daga yammacin Alhamis a filin paretin sojoji na shalkwatar da ke Mogadishu Cantonment, Abuja.
A ranar Juma’a da safe ne za a gudanar da babban taron jana’iza a Cibiyar Kiristoci ta Kasa (National Christian Centre) kafin a binne gawarsa a makabartar sojoji ta kasa da ke Abuja da yamma.
A makon da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta sanar da rasuwar Lagbaja a Legas bayan wata gajeruwar rashin lafiya.
Marigayin, wanda aka haifa a ranar 28 ga watan Fabrairu, 1968, ya rike mukamin babban hafsan sojin kasa na Najeriya tsawon shekara daya da wata hudu, tun bayan da aka nada shi a watan Yuni na 2023.
Lagbaja ya taka muhimmiyar rawa a wasu manyan ayyukan tsaro a fadin kasar, ciki har da Operation ZAKI a Jihar Benuwe, Lafiya Dole a Jihar Borno, Udoka a yankin kudu maso gabas, da kuma Operation Forest Sanity a jihohin Kaduna da Neja.
Marigayi Laftanar Janar Lagbaja ya fara aiki da rundunar sojin Najeriya tun bayan da ya shiga makarantar horar da sojoji ta NDA a shekarar 1987, inda aka nada shi Laftanar Soja a bangaren Infantry a shekarar 1992.
A tsawon aikinsa, ya shugabanci dakaru daban-daban, ciki har da gungun Battalion na 93 da 72 Special Forces Battalion.
Ya kasance cikakken dalibi a makarantar sojin kasar Amurka (U.S. Army War College), inda ya samu digirin digirgir a kan tsare-tsaren dabarun soja, wanda hakan ya kara masa kwarewa a harkokin jagoranci. Marigayin ya rasu ya bar mata, Mariya, da ’ya’ya biyu.
Shugaba Bola Tinubu ya aiko sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da dukan rundunar sojin Najeriya, yana mai bayyana cewa Najeriya ta yi babban rashin jajirtaccen hafsan soja da ya sadaukar da rayuwarsa don tsaron kasa da zaman lafiya.
Dandalin Mu Tattauna