Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Daga Mukamin Babban Hafsan Sojan Najeriya Na Riko Zuwa Laftanar Janar


Kakakin fadar shugaban kasa Bayo Onanuga ne ya tabbatar da faruwar lamarin da ya gudana a fadar shugaban kasar.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya daga likkafar Babban Hafsan Sojan Najeriya na riko Olufemi Oluyede zuwa laftanar janar.

Kakakin fadar shugaban kasa Bayo Onanuga ne ya tabbatar da faruwar lamarin da ya gudana a fadar shugaban kasar.

Matukar Majalisar Dattawa ta tabbatar da shi zai kasance cikakken babban hafsan sojan Najeriya da zai maye gurbin Laftanar Janar Taoreed Lagbaja a mataki na dindindin.

An daga likkafar babban hafsan sojan Najeriya ne kwanaki bayan da Shugaba Tinubu ya nada shi akan mukamin a mataki na riko.

A nasa bangaren, Laftanar Janar Oluyede ya bayyana matukar godiya tare da martaba lamarin.

Ya jaddada aniyar dabbaka muradan Laftanar Janar Taoreed Lagbaja tare da tabbatar da zaman lafiya a fadin Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG