Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Hafsan Sojin Najeriya Taoreed Lagbaja Ya Rasu


Lagbaja Ya Zama Cikakken Janaral Mai Tauraro Uku
Lagbaja Ya Zama Cikakken Janaral Mai Tauraro Uku

Mai bai wa shugaban kasa shawara na kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Laraba.

Fadar Shugaban kasa ta sanar da mutuwar Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja bayan wata gajeruwar jinya a Legas ya na da shekaru 56.

Mai bai wa shugaban kasa shawara na kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Laraba.

A wata sanarwa da kakakin fadar shugaban kasar, Bayo Onanuga, ya fitar Shugaban ya jajantawa iyalinsa da Rundunar Sojin Najeriya baki daya a irin wannan mawuyacin lokaci.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Babban Kwamandan Sojoji, na nadamar sanar da Rasuwar Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, Shugaban Hafsan Sojin ƙasa yana da shekaru 56.”

Hakan na zuwa ne bayan da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya daga likkafar Babban Hafsan Sojan Najeriya na riko Olufemi Oluyede zuwa laftanar janar.

An daga likkafar ne kwanaki bayan da Shugaba Tinubu ya nada shi a kan mukamin a mataki na riko.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG