Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Nada Mukaddashin Babban Hafsan Sojin Najeriya


Manjo Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede
Manjo Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede

Mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya ce Olufemi zai ci gaba da rike mukamin har lokacin da Janar Taoreed Lagbaja zai dawo kasar.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nada Manjo Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede a matsayin Babban Hafsan Sojin kasar na riko.

Mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya ce Olufemi zai ci gaba da rike mukamin har lokacin da Janar Taoreed Lagbaja zai dawo kasar.

Kafin nadinsa, Oluyede ya kasance Kwamandan rundunar zaratan askarawan sojan Najeriya na 56 dake Jaji, a jihar Kaduna

A ranar 21 ga watan Oktoba da muke ciki ne Rundunar sojin Najeriya ta yi fatali da rade-radin da ake yi cewa Babban Hafsan Sojin Kasa Laftanar Janar Taoreed A. Lagbaja ya rasu.

A wani rubutu da ta yi da manyan haruffa akan wani labarin da aka wallafa a shafin X a ranar Lahadi, rundunar sojin ta Najeriya ta ce “Labarin na boge ne.”

Tushen labarin kamar yadda kafafen yada labaran Najeriya suka ruwaito daga Jackson Ude ne, wani tsohon hadimin shugaban kasa kuma mai sharhi a kafafen sada zumunta.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG