Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Farmaki Ta Sama Kan 'Yan Boko Haram Aka Kashe 10


Sojojin Najeriya a cikin wani wurin da hukumomi suka ce a baya, babban sansani ne na 'yan Boko Haram a kusa da Konduga a Jihar Borno
Sojojin Najeriya a cikin wani wurin da hukumomi suka ce a baya, babban sansani ne na 'yan Boko Haram a kusa da Konduga a Jihar Borno

Sojojin Najeriya sun ce sun kashe 'yan Boko Haram su 10 lokacin da suka bi sawun 'yan kungiyar dake tserewa bayan lalata sansanoninsu biyu a kusa da Konduga

Sojojin gwamnatin Najeriya sun kai hare-hare ta sama, sannan daga bisani suka kashe 'ya'yan kungiyar nan ta Boko Haram su 10 a yankin arewa maso gabashin kasar mai fama da fitina.

Rundunar sojojin Najeeriya ta fada jiya laraba cewa mayakanta sun gwabza fada da "'Yan ta'addar Boko Haram" dake tserewa a bayan da aka ragargaza wasu sansanoninsu guda biyu dake kusa da garin Konduga a Jihar Borno.

Babu wani cikakken bayanin da aka bayar game da wadannan hare-hare da aka kai ta sama a kan sansanonin. A can baya dai, mayakan Najeriya sun yi amfani da jiragen saman yaki wajen kai farmaki a kan wuraren da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram sun buya ko sun kafa sansani tun daga cikin watan Mayu, a wani yunkurin kawo karshen zub da jinin da suke haddasawa.

Kakakin rundunar hadin guiwa ta tsaro, JTF, a jihar Borno, leftana-kanar Sagir Musa, ya fada cikin wata sanarwar da ya bayar cewa arangamar da aka yi da 'yan Boko Haram, ta biyo bayan kai hari ta sama tare da lalata wasu sansanoni biyu a Mada, yankin karamar hukumar Konduga.
Ya ce, "an kashe 'yan ta'adda 10, an kuma samu makamai da albarusai, ciki har da bindigogin kai farmaki kirar AK-47 guda 4, da kunshin jigidar harsasai na AK-47 guda 5, da kuma harsasai dabam-dabam guda 250."

An sha ganin tashin hankali da zub da jini a yankin na Konduga. A ranakun 10 da 11 ga watan Agusta, wasu mutanen da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun abka cikin wani Masallaci a Konduga, suka kashe masallata 44, da kuma mutane 12 a wani kauyen dake nan kusa.

Akasarin hare-hare da zub da jinin da kungiyar Boko Haram ke yi a baya-bayan nan, ramuwar gayya ce da suke kaiwa a kan fararen hula na garuruwa da kauyukan yankin a saboda kakkafa kungiyoyin banga da suka yi su na taimakawa hukuma wajen bin sawu tare da kamo 'yan Boko Haram.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG