Wani kakakin sojojin Najeriya, Kanar Sagir Musa, ya fada yau asabar cewa dakarun sun bi sawun 'yan bindigar ne a bayan da mayakan Boko Haram suka kashe mutane 20 a wasu hare-hare ranakun laraba da alhamis a wasu kauyukan Borno.
Kanar Sagir ya ce, "sojoji sun bi 'yan ta'addar zuwa cikin sansanoninsu, kuma tare da tallafin jiragen saman yaki, an kashe 'yan ta'adda guda 50 a fadan da aka gwabza."
Kungiyar Boko Haram, wadda ta yi ikirarin cewa tana so ne ta kafa tsarin shari'ar Musulunci a yankin arewacin Najeriya, da wasu kungiyoyin masu alaka da ita, sune ke haddasa barazanar tsaro mafi muni ga Najeriya, kasar da ta fi arzikin man fetur a Afirka.
Sai dai kuma al'ummar Jihar Borno da ma kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun yi zargin cewa sojoji su kan kara gishiri a irin nasarorin da suka samu tare da rage yawan dakarunsu da aka kashe ko fararen hula.