WASHINGTON, DC —
Dubban mutanen garin Kajuru dake Jihar Kaduna a arewacin Najeriya, sun yi zanga-zangar nuna rashin jin dadin abinda suka kira kame-kamen babu-gaira-babu-dalili da 'yan sanda keyi, a bayan da aka kashe 'yan sanda uku a wani hari kan hedkwatarsu makonni biyu da suka shige.
Wani mazaunin garin yace an kama mutane biyu kan babur ranar asabar, sannan kuma a jiya talata, 'yan sanda sun damke karin mutane 7 daga gidajensu.
Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Kaduna, Aminu Lawan, yace kame wadannan mutane da aka yi yana da nasaba da farmakin da aka kai a kan hedkwatar 'yan sandan Kajuru a ranar 20 ga watan Agusta. Yace mutanen Kajuru sun kuma mika wasu karin mutane guda biyu wadanda suke taimakawa wajen gudanar da bincike.
'Yan sanda sun ce mahara dauke da muggan makamai sun saki wasu barayi da 'yan fashin da aka kama ana tsare da su a ofishin 'yan sandan.
Talata, 'yan zanga-zanga sun toshe hanyar shiga garin Kajuru. An tura 'yan sanda da sojoji cikin damarar yaki sosai zuwa yankin, amma ba a samu wani rahoton fada ko tashin hankali ba.