A baya, rundunar ta koka da rashin samun hadin kan farar hula, musamman wajen samun bayanan sirri da zasu taimaka wajen bin sawun masu tayar da fitina ko barazana ga tsaro da zaman lafiyar kasa.
Birgediya Janar Christian Oluwaku, babban kwamandan birged ta 31 ta mayakan Najeriya dake Minna a Jihar Neja, ya yaba da wannan ci gaban da aka samu, yana mai bayyana shi a zaman abin farin ciki wanda kuma zai kawo cimma nasarar gurin tabbatar da tsaro a kasa.
Birgediya janar Oluwaku yayi misali da abubuwan dake wakana a yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda fararen hula 'yan banga da ake kira “Civilian JTF” a turance, suka mike da sanduna da adduna su na tinkarar 'yan bindigar dake rike da muggan makamai, a saboda sun tunzura, sun kawo wuya da irin cin zarafi sa rashin imanin da 'yan bindigar ke nunawa.
Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari, ya aiko mana da karin bayani.