Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yansanda Sun Kai Hari Kan Dogarawan Gombe


Mota da aka farfasa
Mota da aka farfasa

Jihar Gombe na daya daga cikin jihohin da suka kafa dogarawa da suke yin sintiri a hanyoyi domin tsare lafiya.

Dakarun 'yansandan Gombe sun farma dogarawan da gwamnati ta kafa masu yin sintiri domin tabbatar da tsaro.

To amma da alama 'yansanda basu saba da ganin dogarawan ba domin jiya sun farmasu yayin da dogarawan ke sintiri a kan hanya cikin dare. Shugaban dogarawan Malam Babaji Hassan Dunama shi ya bayyana harin da 'yansanda suka kaiwa dakarunsa bayan ya kubutosu daga hekwatar 'yansandan jihar. Yace jami'in 'yansanda mai kula da garin Gombe shi ya turo yaransa suka kawo ma dogarawan hari. Malam Babaji ya ce wajejen karfe tara na dare ya fita ya ga yaransa da yadda suke aiki sai ya ga motar 'yansanda ta gicciye hanya 'yansandan rike da bindigogi suna hayaniya da yaransa. Ya ce 'yansandan sun bubuge kan yaransa suna jini. Ko a gabansa sun buge kan wani. Daga bisani suka dauki motarsu suka tukata zuwa ofishinsu na 'yansanda. Shi ma Malam Babaji bai tsira ba domin sun fasa motarsa sun yaga littafan yaransa dake cikin motar. A cewarsa da kyar ya sha.

Mai magana da yawun 'yansandan Faje Attajiri ya ce tun farko inda Malam Babaji na cikin kayan sarki da hakan bai faru ba ko kuma da ya nuna katin shaidar inda yake aiki.Ya ce an yi wannan abun cikin kuskure domin ba'a san dogarawan jami'an gwamnati ba ne. Ya ce za'a binciki abun da ya faru duk dansandan da ya yi ba daidai ba za'a hukuntashi.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG